Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Jaridar Egypt Today ta nakalto jakadan kasar Korea ta Kudu a masar Hong Jin-Wook yana fadar haka a jiya Litinin, a lokacinda ya kai ziyarar ganin kamfanin kera talabijin na ‘Beni Suel’ da ke birnin Alkahiram inda ake saran za’a kafa kamfanin komfutoci na Samson.
Labarin ya kara da cewa ministan sadarwa Amr Tala’at da kuma ministan ilmi na tare da jakadan a lokacinda ya kai ziyara a kamfanin na Bene Suel’ . Wannan dai shi ne kamfanin kera komfutoci na farko wanda Samsun zai bude a nahiyar Afirka.
Banda haka komfutoshin Samsun kirar masar dai za su zama wani nau'in kayakin Samson ne, wanda kuma za’a saida su tare hadin kai da kamfanin Samsun na Korea ta Kudu da Masar da kuma duk wata kasa da za ta saye kumfutocin.
342/